Tsohon Majalisar Dattawa Dino Melaye ya bai wa Majalisar Tarayyar Najeriya wa’adin kwanaki 14 ta ɗauki matakan da za su tabbatar da sa ido kan ikon Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ko kuma ya jagoranci zanga-zanga a harabar majalisar.
Melaye, wanda ke cikin jagororin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Ya zargi Majalisar Tarayya ta 10 da gaza sauke nauyin da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora mata na sanya ido kan ayyukan ɓangaren zartarwa na gwamnati.
Tsohon sanatan ya kuma soki yadda majalisar ta tafiyar da wasu batutuwa da suka shafi gyaran dokokin zaɓe, dokokin ’yan sanda, dokokin haraji da kuma ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers.
Melaye ya bayyana cewa ya kamata ’yan majalisar su tabbatar da ’yancin cin gashin kansu wajen gudanar da ayyukansu.
Ya yi gargaɗin cewa idan majalisar ba ta ɗauki matakan da ya buƙata cikin kwanaki 14 ba, zai jagoranci zanga-zangar da ya kira “Occupy National Assembly” domin nuna rashin gamsuwa da yadda majalisar ke gudanar da ayyukanta.
