Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada cewa Ilimi ne kan gaba cikin abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba, tare da shan alwashin ci gaba da zuba jari a fannin domin bunkasa ilimin ɗan Adam da ci gaban jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin haɗin gwiwar yaye ɗaliban Jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila, inda ɗalibai sama da dubu ɗaya suka kammala karatu tare da samun shaidun digiri daban-daban.
Abba ya ce muhimmancin da gwamnatinsa ke baiwa ilimi ya bayyana a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, inda fannin ilimi ya samu kaso mafi tsoka, tare da yabawa Jami’ar ta Al-Istiqama bisa gudunmawar da take bayarwa wajen samar da damar ilimi ga matasa.
A nasa jawabin, mamallakin jami’ar, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, ya ce manufar kafa jami’ar ita ce samar da ingantaccen ilimi mai nagarta da tarbiyya, musamman ga al’ummar yankunan karkara.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sanatan na godewa masu ruwa da tsaki da ma’aikata da ɗalibai bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jami’ar.
