
Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya sanar da amincewa nan take da tsarin albashi na matakin tarayya ga duk ma’aikatan lafiya a jihar.
Gwamman ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin bikin bude taron farko na kiwon lafiya na Gombe, wanda aka yi a Cibiyar Taro ta Duniya ta Gombe.
Jihar za ta rungumi tsarin Consolidated Medical Salary Structure (CONMESS) ga likitoci da Consolidated Health Salary Structure (CONHESS) ga ma’aikatan jinya, ungozoma, da sauran ma’aikatan lafiya, wanda ya dace da ka’idodin tarayya.
Wannan shiri zai lakume kusan Naira biliyan 3 a shekara.
Wannan mataki na matsayin “saka jari kai tsaye a cikin jin dadin ma’aikatan lafiyarmu” in ji shi.
Gwamna ya bukaci ma’aikatan lafiya da su mayar da hankali tare da jajircewa da inganta aiki don bunkasa fannin lafiyar ga jama’a.
Masana sun yaba wa wannan mataki da gwamnan ya dauka saboda abu ne mai muhimmanci don magance kalubalen sashen lafiya, ciki har da
Albashin da ya dace na tarayya wanda zai iya taimakawa wajen riƙe ƙwararrun ma’aikata da kuma hana ƙaura zuwa wasu Jihohi da Kuma kasashen waje.
Hakan Kuma zai iya jawo ƙarin ƙwararrun ma’aikata zuwa yankunan karkara da marasa galihu, wanda zai ƙarfafa harkokin lafiya a jihar baki daya