An sako matafiya 28 da aka yi garkuwa da su a hanyar zuwa taron Maulidi a garin Zak da ke yankin Bashar a Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
A ranar 21 ga Disamba, 2025, ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Zak da ke yankin Bashar a Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
Mutanen da aka sace suna kan hanyarsu ta zuwa garin Sabon Layi, a yankin Bashar din, domin halartar bikin Mauludi, lokacin da aka tare su aka yi garkuwa da su.
Bayan sace su, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi ’yan uwansu, suna buƙatar a biya kuɗin fansa na Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum. ’Yan uwan sun ce ba su da ikon biyan kuɗin, suka roki a sako mutanen.
- ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu A Harin Kasuwar Canjin Kuɗi A Sakkwato
- ’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 a Jihar Filato
- Yaki da ‘yan bindiga: Gwamnan Kano ya ba sojoji motoci 10 da babura 60
Daga baya masu garkuwa da mutanen sun rage kuɗin fansar zuwa Naira miliyan 30, amma suka ƙara bukatar a kawo sabbin babura uku kacal.
A ranar Alhamis kuma, iyalan wadanda aka sace sun ce masu garkuwa da mutanen sun sake sauya sharadi, inda suka buƙaci Naira miliyan 1.5 da kuma sabuwar babur daya kan kowane mutum kafin sakin su.
Da yake tabbatar da sakin mutanen, wani shugaban matasa a Karamar Hukumar Wase, Sapi’i Sambo, ya ce Jami’an DSS ne suka kirawo su da dare suka sanar da cewa sun kuɓutar da mutanen.
Har yanzu ba a tabbatar da ko an biya kuɗin fansa ba, sai dai iyaye sun ce ko sisin kwabo ba su biya ba.
