Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na ƙasa domin zaɓen sabbin shugabanni ba.
wannan na cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na PDP, Debo Ologunagba, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa PDP ta yi mamakin hukuncin da Alƙali Kolawole Omotosho ya yanke, tare da bayyana shi a matsayin yunƙurin take tsarin dimokuraɗiyya.
- Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
- Lamido hayaniya yake yi don jan hankali ba neman takara ba – PDP
PDP ta ce za ta ci gaba da shirye-shiryen taronta na ƙasa don zaɓen shugabannin jam’iyyar na gaba, tare da tabbatar da bin doka da tsari, yayin da lauyoyinta ke shirin daukaka ƙara kan hukuncin.
