Cibiyar Ƙasa da Ƙasa mai Kula da Hijira (IOM) ta ce ta taimaka wajen dawo da sama da ’yan Najeriya 70,600 da suka yi hijira zuwa ƙasashen ketare ta hanyoyin da ba su dace ba, tun daga shekarar 2017 zuwa yanzu.
Cibiyar ta bayyana hakan ne yayin wani taron kwana biyu da aka shirya domin wayar da kan ’yan jarida da masu gabatar da shirye-shiryen rediyo kan matsalolin hijira ba bisa ka’ida ba da safarar mutane, wanda aka gudanar a Kano.
Jami’in Sadarwa na IOM Nigeria, Elijah Alaigwu, ya ce sama da 44,500 daga cikin waɗanda suka dawo sun samu tallafin sake farfadowa da komawa cikin al’umma, yayin da ake ci gaba da taimaka wa wasu.
Ya ce IOM ba ta hana ’yan Najeriya tafiya ƙasashen waje ba, sai dai ta shawarci masu shirin yin hakan da su bi hanyoyin doka tare da samun cikakkun takardu, domin kauce wa fadawa hannun masu safarar mutane da masu safarar bakin haure.
A nasa bangaren, Umar Muhammad, Shugaban Sashen Wayar da Kan Jama’a na NAPTIP, Kano Zonal Command, ya ce hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 154 tun daga watan Janairu zuwa yanzu, waɗanda suka shafi safarar mutane, bautar da yara, cin zarafin yara da sauran nau’o’in amfani da mutane ba bisa ka’ida ba.
Ya ce hukumar ta samu hukunci tara a wasu daga cikin shari’o’in, inda wasu daga cikin waɗanda aka samu da laifi aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na tsakanin shekara shida zuwa bakwai.
Umar Muhammad ya bayyana Kano a matsayin muhimmiyar hanyar wucewar masu safarar mutane, saboda matsayinta da kusancinta da wasu jihohi da kuma iyakokin ƙasa.
Ya ce NAPTIP da IOM na haɗin gwiwa wajen gano tare da tallafa wa waɗanda aka yi safarar su, da kuma ’yan Najeriya da suka dawo daga tafiye-tafiyen hijira ba bisa ka’ida ba.
Jami’in NAPTIP ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara wayar da kan jama’a kan illolin hijira ba bisa ka’ida ba, domin rage yawan mutanen da ke fadawa hannun masu safarar mutane da masu safarar bakin haure.
