Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta sanar cewa jami’anta sun murƙushe wata ƙungiyar da ake zargi da safarar makamai a Jihar Gombe, tare da kama mutane biyu da ake zargi, da kuma kwato makamai masu haɗari ciki har da rokoki na RPG.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa an cafke Muhammed Alhaji Mohammed mai shekaru 55 da Sani Gesha mai shekaru 47 a Mararaban Tula da ke Ƙaramar Hukumar Kaltungo, yayin da suke tafiya cikin wata mota kirar Toyota Corolla mai launin toka, mai lambar Taraba JAL475YQ.
Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da kananan rokoki biyu na RPG, na’urar harba rokoki da sauran makamai.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa kamen ya biyo bayan makonni uku na sa ido a ɓoye kan wata babbar hanyar safarar makamai a jihohin Bauchi, Gombe, Taraba da Adamawa.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu a yayin tambayoyi, inda suka ce makaman za a kai su ne zuwa wani mutum a ƙauyen Kukawa da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi.
A wani cigaban mai alaƙa da wannan, jami’an DSS sun kuma ceto wani yaro ɗan shekara shida mai suna Mohammed Jabir, wanda ake zargin an yaudare shi tare da sace shi da sunan koya masa babur.
An kama wanda ake zargi, Salisu Hussain, dangane da lamarin, yayin da aka miƙa yaron ga iyayensa cikin farin ciki.
Hukumar ta ce duk waɗanda ake zargi suna hannunta, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
