Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sake jaddada cikakken shiri na fara jigilar maniyyata aikin hajji bana zuwa Ƙasa Mai tsarki domin gudanar da aikin hajji na wannan shekarar
Shugaban Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, jim kaɗan bayan ƙaddamar da shirin allurar rigakafi ga maniyyata a Asibitin sansanin Alhazai dake nan Kano.
Alhaji Abubakar Matawalle ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar kammala bayar da biza ga dukkan maniyyatan aikin hajji bana, yana mai cewa wannan nasara nada alaka ne da ƙudurin Gwamnatin Jihar Kano wajen samar da ingantattun ayyuka da kuma kula da jin daɗin maniyatan.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar da aikin Hajji mai sauƙi da cike da armashi na ibada ga dukkan maniyyatan jihar.
A na ta jawabin, Daraktar a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya Dakta Bilkisu Jibiril Idris ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da shugabancin Hukumar Jin Daɗin Alhazai bisa kyakkyawan tsari da bin ƙa’idojin lafiya.
Inda ta bayyana shirin rigakafin a matsayin abin koyi, tana mai cewa Kano ta fi sauran jihohin da ta ziyarta tsari, haɗin kai da ƙwarewa a yayin da ake gudanar da allurar rigakafi ga maniyata.
