Gwamnatin Kano ta fito da wani shiri da manufar ci gaban karkara na tsawon shekaru biyar, wanda zai shafi ƙananan hukumomi 44 na jihar daga shekarar 2026 zuwa 2030.
Kwamishinan Ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma na Kano, Dr Abdulkadir Abdussalam, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai domin bayyana shirye-shiryen gwamnati kan bunƙasa karkara mai ɗorewa.
Dr Abdul Salam ya ce a shekarar 2025 ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci ma’aikatar ta gudanar da bincike a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar domin tantance muhimman buƙatun al’ummomin karkara, musamman a fannonin hanyoyi, gine-ginen more rayuwa da sauran muhimman abubuwan ci gaba.
A cewarsa, gwamnatin jihar za ta ƙaddamar da shirin ne a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, yayin da a ranar Talata, 30 ga watan Yuni, 2026, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai ƙaddamar da kwamitin da zai sa’ido kan aiwatar da shirin.
