Ƙungiyar Ansaru, mai alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda, ta ɗauki alhakin kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, tare da zarginsa da kasancewa kafiri.
Masanin harkokin tsaro, Audu Bulama Bukarti ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a Facebook, inda ya ce ƙungiyar ta tabbatar da ɗaukar alhakin kisan ta hanyar wani saƙon murya da ta fitar.
A cewar bayanin, Ansaru ta ce ta kai harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare. Sai dai, akwai rashin daidaito a cikin saƙon game da ranar da harin ya faru.
Bukarti ya bayyana cewa ƙungiyar ta zargi malamin da adawa da Musulunci, amma ba ta bayyana wani takamaiman laifi da ya aikata ba.
Ya kuma yi nuni da cewa matsayar Sheikh Yahaya Masussuka kan tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban da ƙarfafa zaman lafiya na iya kasancewa cikin abubuwan da suka jawo harin, duk da cewa ba a tabbatar da wannan a matsayin dalilin kisan ba.
Ansaru ta balle daga Boko Haram a shekarar 2012, bayan rashin jituwa da shugabancin Abubakar Shekau, kuma an danganta ayyukanta da wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya.
