Dakarun sojin Najeriya da ke gudanar da aikin Operation Fansan Yamma sun gano tare da lalata bama-bamai guda biyu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka dasa a kan hanyar Magami zuwa Dansadau, a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Dakarun sun gano bama-baman ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan abubuwan fashewar da aka dasa domin kai hari ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar.
Bayan samun bayanan, sojojin sun fara tabbatar da tsaron yankin kafin gudanar da bincike mai zurfi, wanda ya kai ga gano wurare biyu da aka dasa abubuwan fashewar.
Daga nan ne aka tura tawagar ƙwararru kan lalata bama-bamai domin kawar da barazanar.
Tawagar ta lalata bam guda ɗaya, sannan ta kwato ɗayan cikin aminci tare da kwance shi, ta yadda ba zai iya fashewa ba.
Rundunar sojin ta ce ta ƙara tsaurara sintiri da sa ido a yankin domin kare rayukan mazauna yankin da masu amfani da hanyar, tare da hana sake aukuwar irin wannan barazana.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa a muhallansu, tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro mafi kusa idan suka lura da wani abu ko motsi da suke zargi.
