
Dan wasan gaba na ƙungiyar Paris Saint-Germain (PSG) da ƙasar Faransa, Ousmane Dembélé, ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a wani biki na musamman da aka gudanar daren jiya Litinin a ɗakin taro na Theatre du Châtelet a birnin Paris, Faransa.
Ballon d’Or kyauta ce da akan baiwa ɗan wasan da ya burge a kowace shekara, inda akan yi la’akari da gudunmawar da ɗanwasan ya bayar ga ƙungiya da kuma ƙasarsa.
Kafin bayyanar wanda ya lashe kyautar, hukumar da ke kula da lambar yabo ta fitar da sunan ‘yan wasa 30 da ake sa ran za su lashe kyautar.
Dembele ya buga wasa 53 a kakar bara, inda a ciki ya taka leda na minti 3,483.
Ɗan’wasan na Faransa ya zura ƙwallo 35, sannan ya taimaka aka ci ƙwallo 14 a kakar baki ɗaya.
Lamine Yamal ya zo na biyu a kyautar, bayan da ya lashe ta gwarzon matashin ɗanwasan kyautar a 2025.
Yamal ya buga wasa 55, inda a ciki ya yi wasa na minti 4,548, sannan ya zura ƙwallo 18, ya kuma taimaka aka ci ƙwallo 21, yana cikin waɗanda suka taimakawa ƙungiyar Barcelona ta lashe kofuna uku ciki har da La Liga.
Asalin Ousmane Denbele
An haifi Ousamane Denbele mai cikakken suna Masour Ousmane Dembele a ranar 15 ga watan Mayu ta shekarar 1997 a birnin Vernon, na kasar Faransa… Babarsa ruwa biyu ce ( Mauritanian – Senegalese) Babansa mtumin kasar Mali ne
Ya fara wasan kwallon kafa tun yana yaro a Evreux… Ya shiga kungiyar kwallon kafa ta Rennes a ranar 6 ga wata Nuwanba ta shekarar 2015 ya fara kwallon ta kwarewa a matakin farko… A rana 12 ga watan Mayu ya saka hannu a kwantaragi na shekara biyar da Borussia Dortmund … Da haka ya ci gaba da sana’ar murza leda, wato kwallon kafa…Ya auri Rima Edbouche, yar kasar Marrocco, suna da diya.
Kyauta Ballon d’ Or
Kyautar Ballon d’ Or wacce take nufin Golden ball da turanci, kyauta ce ta kwallon zinare da hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Faransa ta take bawa zakakurin dan wasan kwallon kafa a karshen kakar wasa, la’akari da bajinta, kwarewa da ficen da dan wasa ya yi, a matsayin girmamawa… An fara bada wannan kyauta ne a shekara 1956…Kuma Leon Messi ne ya fi kowane dan wasa samin wannan kyauta, wanda ya karbe ta har sau takwas.