Saurari premier Radio
23.1 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiBa mu umarci NNPCL ya kara farashin mai zuwa N1,000 ba –Gwamnatin...

Ba mu umarci NNPCL ya kara farashin mai zuwa N1,000 ba –Gwamnatin tarayya.

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce bata bawa kamfanin NNPCL umarnin kara farashin man fetur zuwa N1,000 ba.

Karamin Ministan man fetur Heineken Lokpobiri ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Nnemaka Okafor.

Ministan yace ba gwamnatin tarayya ce ta tilastawa kamfanin NNPCL kara kudin mai ba, domin kuwa NNPCL kamfani ne mai zaman kansa, wanda yake aiki kan tsarin dokar kamfanoni.

Ya kara da cewa batun karin kudin man fetur maganar cikin gida ce a NNPCL, don haka batun bai shafi gwamnatin tarayya ba.

Karamin mimistan na man fetur ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da labaran da ke yawo cewa gwamnatin tarayya na da hannu wajen karin farashin man fetur.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...