
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar tafiyar matasa forum ta karrama Dakta Gwani Farouk bisa jajircewarsa wajen hidimtawa al’umma da samar da cigaba a jihar Kano.
Kungiyar wacce ke da ofis a Abuja ta ce ta zabo shi ne a cikin mutane fiye da 100 domin karrama shi.
Ta kuma amince da nada shi a matsayin daya daga cikin iyayen kungiyar na kasa.

Umar Nuhu Tahir shugaban Tafiyar Matasa, reshen Kano, ya ce matasa ne suka fi amfana da irin aiyukan alheri da Dakta Gwani Umar Farouk ya gudanar a rayuwarsa.
Ya ce ya bayar da gudunmawa wajen bunkasa ilimi da samar da sana’o’in dogaro da kai ga dubban al’umma a kasar nan. wanda hakan ne yasa suka zabo shi domin karramawa.
Kwamandan Civilian JTF na jihar Kano Umar Ahmad Baba, ya ce an samar da kungiyar ne a jihar Kano don karfafa harkokin tsaro.
Ya ce wasu jihohin na kirkirar kungiyar idan sun samu matsala amma sun zabi su kirkireta a Kano domin tallafawa hukumomin tsaro.
Ya ce a yanzu suna da ofisoshi 65 a jihar nan yayinda suke da mambobi fiye da 2,500.
Kwamanda Umar Ahmad Baba, ya ce kungiyar tuntubar ta Arewa karkashin Dakta Goni Umar Farouk ta tallafa musu da kayan aiki da horaswa da kudi da yakai kimanin naira bikiyan daya.
A nasa jawabin Dakta Goni Umar Farouk ya godewa kungiyoyin bisa karrama shi da suka yi.
Ya ce zai cigaba da tallafa musu a kowane mataki domin kawo cigaba da zaman lafiya a jihar Kano da Najeriya baki daya.
Dakta Gwani Farouk ya ce karramawar da aka yi masa zata kara masa kwarin gwiwa na cigaba da aiwatar da aiyukan cigaba.
