Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya sarkin musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin musulunci a Najeriya, mai alfarma Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na Uku, murnar cika shekaru 70 da haihuwa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana Sarkin Musulmin a matsayin jagoran addini da na gargajiya mai matuƙar kima, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna a Najeriya.
Gwamnan Abba ya yaba da hikima da tawali’u da kuma jajircewar Sarkin Musulmin wajen kula da harkokin al’ummar Musulmi, musamman ƙoƙarinsa na ƙarfafa haɗin kan Musulmi da samar da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa jagorancinsa a Masarautar Sakkwato da kuma Majalisar Koli ta harkokin musulunci ta Najeriya ya ci gaba da bayar da jagoranci kan manyan batutuwan da suka shafi ƙasa, musamman zaman lafiya, tsaro da ci gaban Najeriya.
