

Gwamnatin jihar Bauchi ta buɗe ƙofar karɓar bukatun al’ummomi masu sha’awar kafa sabbin masarautu da kuma gundumomi a faɗin jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Kwamared Mukhtar Gidado, ya fitar, inda ya bayyana cewa gwamnati na buɗe ƙofa ga masu neman a samar da sababbin masarautu ko kuma sabbin gundumomi da su mika ƙorafinsu cikin tsari.
A halin yanzu, jihar Bauchi na da masarautu guda shida – Bauchi, Katagum, Misau, Jama’are, Ningi da Dass.
Sai dai a watan Disamba na shekarar 2024, gwamnatin Bala Mohammed ta amince da ƙirƙirar sabuwar masarauta ta Seyawa wadda za ta kasance da hedikwata a karamar hukumar Tafawa Balewa.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa karɓar takardun neman sabbin masarautu da gundumomi zai gudana daga watan nan Yuni zuwa Talata 8 ga Yuli, 2025.