Ahmed Abubakar Zakka, matarsa da jaririyarsu mai watanni shida, Fatima, sun samu ’yanci bayan da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna.
An yi garkuwa da iyalan ne a ranar 6 ga Oktoba, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari a gidansu da ke Alrahus Estate, Millennium City, a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.
Lamarin ya ja hankalin jama’a bayan bayyanar video a shafukan sada zumunta, wanda aka ga Zakka yana riƙe da jaririyarsa yayin da yake roƙon jama’a su taimaka wajen kuɓutar da su daga hannun masu garkuwar.
A cikin bidiyon, Zakka ya bayyana cewa masu garkuwar suna neman kuɗin fansa har Naira miliyan 300 domin sakin iyalansa. Lamarin ya kuma jawo kiraye-kirayen a gaggauta ceto su daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.
Sai dai, rahoton da ya tabbatar da sakin iyalan bai bayyana cikakken bayani kan yadda aka kuɓutar da su ba, ko ko an biya kuɗin fansa kafin sakin nasu. Samun ’yancinsu ya kawo sauƙi bayan fargabar da ta biyo bayan yaɗuwar bidiyon da ke nuna halin da suke ciki.
