Saurari premier Radio
29 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar kare hakkin dan Adam ta IHRC ta nada Mustapha Kaura, daraktan...

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta IHRC ta nada Mustapha Kaura, daraktan karbar korafe-korafe na Arewa maso Yamma

Date:

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta International Human Rights Commission, ta nada Mustapha Ahmad Kaura a matsayin daraktanta na karbar korafe-korafe a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Babban jami’in kula da ayyukan hukumar a shiyyar Arewa maso Yamma Comrade Bello Gama ne ya tabbatar da nadin cikin wata sanarwa da fitar.

Ya ce nadin ya biyo kwarewar da Mustapha Kaura ke da ita wajen kare hakkin dan adam da kuma muhimmiyar rawar da yake takawa wajen ci gaban kungiyar, da hakan ya sanya shi zama mafi dacewa domin jagorantar sashen kararrakin.

Kafin wannan nadi, Mustapha ya kwashe tsawon lokacin ya na aiki da kungiyar ta International Human Rights Commission, wanda hakan ya damar fahimtar rikice-rikicen da kalubalen da ake fuskanta a Arewa maso Yammacin na Najeriya.

Sabon nadin na Mustapha a matsayin daraktan kararraki na yankin, ya dora masa alhakin karbar korafe-korafen da suka shafi hakkin dan adam, bincike da kuma warware su a Arewa maso Yamma.

An dai haifi Mustapha Ahmad Kaura, a watan Janairun shekarar 1987 a karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina.

Mahaifinshi, shi ne babban limamin masallacin garin Dutsen Ingawa, wanda Mustapha ya fara yin karatu da samun horon rayuwa a gurinsa.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...