Manoma sun fara korafi game da yadda gwamnatocin kasar nan suka yi biris da al’amuransu, duk da ikirarin da su ke yi nayin bakin kokari domin kara habaka fannin noma.
Sun ce a yanayin da ake ciki na damuna, har yanzu wasu gwamnatoci ba su taimaka musu da kayan aikin gona ba.
Shugaban gamayyar kungiyoyin manoma ta kasa AFAN reshen jihar Kano, Abdullahi Ali Maiburodi, ya ce tun cikin watan Afrilu suke nusar da gwamnati da masu fada aji game da hanyoyin inganta samun wadataccen abinci, musamman a wannan lokaci da ake fama da tashin farashin kayan masarufi.
Abdullahi Maiburodi, ya ce bana dai ba su samu komai daga dukkan bangarori na tallafi ba, saboda haka suke kara kira a taimaka musu.
Korafin manoman na zuwa ne yayin da a kwanakin baya gwamnatin Kano ta sanar da yin rabon taki ga manoma a yankunan kananan hukumomin jihar 44.