Hukumar Kula Da Inganci Abinci Da Magunguna NAFDAC ta rufe kasuwar wata kasuwa a jihar Abiya bayan wani sumame.
Hukumar ta yi hakan ne a garin Aba a kasuwar Eziukwu da ke birnin Aba bayan gano kayayyakin da suka lalace na kimanin Naira milyan dubu biyar.
A sanarwar da ta wallafa a ranar Laraba, hukumar ta ce an rufe shaguna dari da hamsin a kasuwar, bayan shafe kwana biyu ana samame a cikinta.
Tawagar jami’an NAFDAC ta bankado manyan wuraren samarwa da raba kayan jabu ne da Kuma wadanda lokacin amfaninsu ya ƙare.
Daraktan shiyyar kudu maso gabas na hukumar Dakta Martins Iluyomade, bayyana kasuwar a matsayin cibiyar sayar da jabun kaya da marasa inganci.
“Hukumar ba za ta lamunci irin wannan dabi’a ba, inda mai jaddada ƙudurin kare lafiyar al’umma tare da ƙoƙarin ganin an magance matsalar samar da jabun kayan da ake fama da ita a kasuwanni”. In ji Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye,
Shugabar ta Kuma nuna takaicin yadda ake ci gaba da wannan hada-hada ba bisa ka’ida ba, duk da yarjejeniyar da aka kulla da shugabannin kasuwar na bankado baragurbin cikinsu.
An yi yarjejeniyar ce a watan Disambar 2023, a cewar sanarwar.