Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa an gano yara sama da 17,000 da suka kamu da cutar nimoniya (Pneumonia), wadda ke shafar huhu da kuma numfashi.
Kwamishinan Lafiyar Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Yaƙi da Cutar Nimoniya da Cutar Siga na Duniya a Kano.
A wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar Lafiya, Nabilusi Abubakar K/Na’isa, ya fitar, kwamishinan ya ce sama da yara 300,000 ne cutar nimoniya ta shafa a faɗin Najeriya a shekarar 2026.
Ya yi gargaɗin cewa cutar na iya zama barazana ga rayukan ƙananan yara, musamman waɗanda ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.
Dakta Yusuf ya ce gwamnatin Kano ta horas da ma’aikatan lafiya kan hanyoyin kula da cututtukan yara, domin inganta ayyukan jinya da rage mace-macen da cutar ke haddasawa.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su riƙa kai yaransu asibiti da zarar sun nuna alamomin rashin lafiya, domin samun kulawa cikin lokaci.
