Saurari premier Radio
27.4 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayya za ta samar da sabon shirin hidimtawa kasa makamancin NYSC...

Gwamnatin tarayya za ta samar da sabon shirin hidimtawa kasa makamancin NYSC ga daliban da suka kammala karatun NCE

Date:

Ma’aikatar matasa da hadin gwiwar ta ilimi ta tarayya, ta ce tana aiki domin gabatar da wani sabon shiri na bayar da horo makamancin na hidimar kasa NYSC ga daliban da suka kammala karatun shaidar malanta ta kasa, wato NCE.

Karamin ministan matasa, Olawande Wisdom, da ya bayyana haka yayin bude shirin koyar da sana’o’i na BEMORE OYO 2024 da aka gudanar a birnin Badin na jihar Oyo, ya ce abun da ma’aikatar ta fi mayar da hankali shi ne bayar da horo ga al’ummar kasa.

Ya ce suna da shirin hidimar kasa ga wadanda suka kammala jami’a, amma babu wani shiri ga wadanda suka kammala NCE da sauran masu shaidar karatu a manyan makarantun ilimi.

Saboda haka ya ce za su samar da wani shiri wanda ba sai mutum ya je wata jiha ba zai iya yin sa.

Ministan ya yabawa Dr. Betty Anyanwu Akeredolu, da ta samar da Shirin BEMORE OYO, bisa gudunmawar da take bayarwa wajen ci gaban yaya mata.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...