Saurari premier Radio
29 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiƳan tawayen M23 sun ƙwace iko da wani gari da ke kusa...

Ƴan tawayen M23 sun ƙwace iko da wani gari da ke kusa da kan iyakar Uganda.

Date:

Rahotanni daga gabashin Kongo na cewa ƴan tawayen M23 sun ƙwace iko da wani gari da ke kusa da kan iyakar Uganda.

Hakan ya faru ne a jiya Asabar, daidai lokacin da wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta wata guda ta zo ƙarshe.

Mazauna garin sun ce dakarun dake goyon bayan gwmanati sun janye daga garin bayan da ƴan tawayen suka shiga garin.

Wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin Kongon da Angola ta shirya tare da sa hannun – Congo da Rwanda, za ta fara aiki yau.

Sai dai ƴan tawayen M23 ɗin sun kafe cewa ba su cikin yarjejeniyar da gwamnatin Kongo da ta Rwanda suka sanya wa hannu a ranar Alhamis.

 

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...