Saurari premier Radio
23.1 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƘaramin Ministan tsaron ƙasar nan ya bada umarnin binciko masu hannu a...

Ƙaramin Ministan tsaron ƙasar nan ya bada umarnin binciko masu hannu a kisan sarkin Gobir.

Date:

Ƙaramin ministan tsaro na kasa, Bello Matawalle ya sha alwashin cewa za a zaƙulo tare da hukunta duk masu hannu a kisan Sarkin Gobir na Gatawa da ke jihar Sokoto, Isa Bawa.

A ranar Laraba ne labarin kisan sarkin ya fito bayan ya kwashe sama da mako uku a hannun ƴan bindiga.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktar ƴaɗa labaran ofishin ministan, Henshaw Ogubike, Matawalle ya yi tir da kisan sarkin, tare da bayyana hakan a matsayin “aikin rashin imani kuma abin da ba za a amince da shi ba.”

Sanarwar ta ce Matawalle ya umarci shugaban hafsoshin tsaron Najeriya ya ƙaddamar da bincike kan kisan nan take tare da tabbatar da ganin an hukunta duk wadanda ke da hannu cikin lamarin.

A jiya Alhamis ne dai aka gudanar da sallar jana’iza ta ‘Salatul Ga’ib’, ga sarkin na Gobir, wanda ƴan bindiga suka hallaka, kasancewar ba a samu gawarsa ba.

Sai dai an samu nasarar karɓo ɗan marigayin, wanda ƴan bindiga suka ce su tare, wanda yanzu haka yake karɓar kulawa a asibiti.

Matsalar masu satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da addabar jihohin arewa maso yammacin kasar nan, duk kuwa da ƙoƙarin da hukumomi suka ce suna yi wajen tabbatar da tsaro.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...