Ƙarancin wutar lantarki ya ƙara tsananta a sassa daban-daban na Najeriya, yayin da jama’a ke fama da ƙaruwar zafi.
Hukumomin samarwa da dakon wutar lantarki sun danganta matsalar da ƙarancin iskar gas da tashoshin samar da wuta ke amfani da ita, da kuma raguwar ruwan kogunan da ake amfani da su wajen samar da lantarki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƙarfin wutar lantarkin da ake samarwa a ƙasar ya ragu zuwa megawat 3,940.
Wannan matsala na ƙara jefa gidaje da ’yan kasuwa cikin ƙalubale, musamman a lokacin da ake buƙatar wutar lantarki domin rage raɗaɗin zafi.
