Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta kama wasu mutane uku da ake zargin su da daukar nauyin yan ta’adda tare da taimaka musu wajen wajan kai hare-hare akan al’ummar jihar Sokoto.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufa’I fitar a jiya juma’a.
- Gwamnati za ta soma ba masu haka Kabari albashi Sokoto
- Gwamnatin Jihar Sokoto ta soke lasisin takardun mallakar gidaje, fili, gonaki a jihar.
- EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Sokoto Tambuwal Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 189
Hakazalika yan sandan sun samu nasarar kwato shanun da aka sace da kuma babura da aka sace a wani aiki na hadin gwiwa tsakanin rundunar sandan da kuma taimakon wasu jami’an tsaro.
Rundunar yan sandan tace ta samu nasarar dakile wani hari da yan ta’addar suka yi yinkurin kaiwa karamar hukumar Tangaza, wanda kuma hakan ya farue sakamakon bayanan sirri da yan sandan suka samu daga wajan al’umma.
