Rundunar yan sandan jihar Sokoto ta kama wasu matasa guda biyu wadanda ake zargin yan wata kungiyar asiri ne da aka fi sani da sai Malam.
Kakakin rundunar yan sandan jihar DSP Ahmad Rufa’I shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci holin mutanan bayan yan sandan sun kama su.
Yace wadanda aka sun hada da AbdulRazaka Salihu da kuma Habibu Sahabi bayan samu rahotanni sirri da al’umma suka bawa yan sandan.
- Rundunar ’Yan Sanda a Kano Ta Dakile Safarar Abubuwan Fashewa Bayan Bayanai na Sirri
- ’Yan Sanda Sun Yi Gargadi Kan Ta’addanci a Kano
- Tinubu Ya Umurci Janyewar ‘Yan Sanda Daga Gadin Manyan Mutane
DSP Ahmad Rufa’I ya kara da cewa, daga kayayyakin da yan sandan suka samu wadanda ake zargin sun hada da kudin na jabu da goraye da layu da sauran kayayyakin da ake zargi na asiri ne.
Rundunar yan sandan tace da zarar ta kammala bincike kan wadanda zargin zata gurfanar dasu a gaban kotu domin fara fuskantar shari’a.
