
Rundunar ta kama mutumin dauke da miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira miliyan 82 a unguwar Rimin Auzinawa.
kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, 27 ga Satumba, 2025.
Sanarwar ta ce, an kama mutumin mai suna Usman Umar, mai shekara 19, bayan samun bayanai kan wata mota dauke da kwalaye da ake zargin ƙwayoyi ne a cikinsu.
A binciken farko, an gano kwalaye 603 na tabar Tramadol da ke dauke da ƙwayoyi 60,300, da kuma kwalaye 299 na Pregabalin da ke dauke da ƙwayoyi 44,850, jimillar darajarsu ta kai Naira miliyan 82.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike don gano sauran mutanen da ke da hannu a safarar.