Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta bayyana cewa tana ci gaba da gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan mutane uku da ake zargi da kisan iyalan Haruna Bashir da ke zaune a unguwar Ɗorayi Chiranci a jihar.
Tuni rundunar ta cafke wasu mutum uku da ake zargi sune suka kashe Fatima da ’ya’yanta 6 jim kaɗan bayan faruwar lamarin.
Kakakin Rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da haka a shafinsa na Facebook inda ya ce binciken ƙwaƙwaf na ci gaba da gudana.
