
Kungiyar magoya bayan Kano Pillars taki amincewa da hukuncin da hukumar shirya gasar gasar Premier ta kasa dauka, bayan hargitsin da aka samu a wasan Kano Pillars da Shooting Stars
A wata tattaunawa ta musamman da jaridar Solacebase, shugaban kungiyar magoya bayan Kano Pillars Rabi’u Abdullahi, ya ce basu gamsu da hukuncin ba, domin an yi musu rashin adalci.
Ya kara da cewa yanke hukuncin cikin kasa da awa 48 ya nuna cewa akwai wata boyayyar manufa akan Kano Pillars.
Abdullahi ya ƙara da cewa ana tuhumar kungiyar da abubuwa guda 9 inda yace wannan ba gaskiya bane, abunda da ake tuhuma akai basu wuce 3 zuwa 4 ba, sauran duk shaci faɗi ne na sauran na hukumar.
Shugaban ya ƙara da cewa suma a nasu bangaren tuni kungiyar ta dauki matakin daukaka ƙara.
NPFL dai ta samu magoya bayan ƙungiyar Kano Pillars da tarun laifukan tada tarzoma ciki harda jifan ƴan wasan kungiyar Shooting stars da abubuwa masu cutarwa.
Haka kuma an ragewa Kano Pillars maki 3 da kuma cin tarar naira miliyan 9.5 da kuma hana ƙungiyar yin wasa a gida dai ta koma jihar Katsina.
Haka zalika hukumar ta bukaci kungiyar ta tabbatar ta nemo wadanda suka tada wannan tashin hankalin, tare da kawo sabbin jami’an tsaron filin wasan ta yanda zasu iya daidaita magoya baya.
Abdullahi dai ya ƙara da cewa hukuncin da aka dauka anyi gaggawa sannan kuma anyi rashin adalci akan kungiyar, sannan kuma yace an yanke hukuncinne ba tare da bincike mai zurfi ba, inda ya tabbatar da daukaka ƙara.