Mataimakin Gwamnan Kano Alhaji Murtala Sule Garo, ya wakilci Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, wajen kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Yayin ziyarar wadda gwamnonin Kasar suka saba kaiwa Tinubu duk lokacin Sallah sun samu damar ganawa da Shugaban da Mataimakinsa tare da cin abincin rana, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban Najeriya, haɗin kan al’umma da kuma zaman lafiya a faɗin ƙasar.
Ganawar ta kuma bawa gwamnonin damar yin musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi muradun ƙasa da hanyoyin da za su ƙara inganta rayuwar al’umma da bunƙasa ci gaban.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Mataimakin Gwamnan na Kano Garo yana jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin shugabanni da kuma al’umma wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaba da kuma wanzuwar Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya.
