Wani marubuci kuma shugaban rukunin jaridun LEADERSHIP, Muazu Elazeh, ya soki matsalar ƙarancin ruwa a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ruwa ya taɓa yankewa yayin da yake aski.
Tinubu ya ba da labarin ne a wani taron addu’a da ‘yan uwansa suka shirya masa a Legas, inda ya bayyana cewa har Fadar Shugaban Ƙasa na fuskantar matsalolin samar da ruwa da wutar lantarki.
Shugaban ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta gyara matsalolin, yana mai cewa ba za a samu ci gaba ba idan babu ruwa da wutar lantarki.
Sai dai a wata maƙala da TheCable ta wallafa, Muazu Elazeh ya nuna mamakinsa kan yadda wasu mahalarta taron suka yi dariya da tafi yayin da shugaban yake bayyana matsalar.
Marubucin ya ce bai kamata a ɗauki matsalar rashin ruwa a Fadar Shugaban Ƙasa a matsayin abin dariya ba, musamman ganin yadda miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da irin wannan matsala.
Ya kuma buƙaci a ɗauki matakan inganta samar da ruwan sha, tare da ba da shawarar amfani da rijiyoyin burtsatse masu aiki da hasken rana a fadar.
Elazeh ya jaddada cewa samar da tsaftataccen ruwan sha nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnatocin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
