(A dama) Kabiru Maikaba da Yakubu Liman ( a hagu) na mikawa Aina'u takardar taya murna daga Gidauniyar Kaannywood a yayin ziyarar
Babbar Mai Taimakawa Gwamnan Kano kan al’amuran Kannywood Hajiya Aina’u Ade ta bayyana aniyarta na hada hannu da Gidauniyar Kannywood don aiki tare domin cigaban masana’antar Kannywood.
Aina’u ta bayyana hakan ne a ranar Litinin a ofishinta, a yayin ziyarar taya murna da wakilan gidauniyar karkashin Kabiru Mai Kaba, Sakateren Gidauniyar, suka kai mata.
A jawabinta a yayin ziyarar, ta bayyana farin cikinta da gidauniyar da kuma yi mata fatan alheri.
“Ina mai matukar murna da wannan ziyara da kuma takardar taya murna da gidauniyar ta aiko ta hannu Babana Maikaba da kuma jami’in hulda da jama’a”.
“Kuma ina mutunta tare da girmama dattawan industry da suka hadu suka kafa wannan kungiya. Zan kuma samu lokaci in zo mu zauna da su don jin shawarwari da nasihohin da za su taimakawa aikina.” In ji ta.
A na shi jawabin Sakataren gidauniyar Malam Kabiru Mai Kaba, ya yaba da nadin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa jarumar.
“Hakika hakan ya dace matuka, la’akari da jajircewar ki da kuma rawar da ki ke takawa a masana’antar Kannywood”. In ji shi.
Mai Kaba ya kuma yi kira a gareta da ta yi amfani da wannan matsayin don kawo cigaba mai alfanu ga masana’antar da kuma jihar Kano baki daya.
Sakateren ya samu rakiya Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a Yakubu Liman a yayin ziyarar.
