Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZamu farfado da kimar Yan Jarida na Nahiyar Afrika tare da tabbatar...

Zamu farfado da kimar Yan Jarida na Nahiyar Afrika tare da tabbatar da Yan Jarida sun samu cikakkiyar walwala a Nahiyar Afrika.

Date:

Zamu farfado da kimar Yan Jarida na Nahiyar Afrika tare da tabbatar da Yan Jarida sun samu cikakkiyar walwala a Nahiyar Afrika.

Hajiya Mariama Laouali Serkin Abzine Niamey Niger itace ta bayyana haka a wajen taron kungiyar hada kan Yan Jarida na kasashen Afrika masu amfani da harshen Hausa Wanda ya gudana a Babban Birnin Niamey na Jamhoriyar Niger.

A yau ne ake karkare babban taron kungiyar yan jaridar kasashen Afrika masu amfani da harshen Hausa wanda yake gudana a Niamey babban Birnin kasar Jamhuriyar Nijar.

Taron dai ya zo ne a wani bangare na kafa kungiyar hadin kan yan jarida na kasashen Africa masu amfani da harshen Hausa domin ganin aikin jarida ya kawo sauyi ga yanki.

Premier Radio dai na daga cikin kafafen yada labarai da suka hakarcin taron wanda shine karo na farko da aka gudanar dan ganin bunkasa harshen Hausa da cigaban tattalin arzikin kasashen Afrika masu amfani da harshen Hausa.

Sai an aza harsashin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da tabbatar da yancin kasashen Africa Wanda aka gudanar a yau a babban birnin Jamhoriyar Niger Yamai.

 

Cikin halartar taron daga Najeriya akwai Major Hamza Almustapha da Hajiya Naja’atu Muhammad da wakilin gwamnan Yobe Baba Gana Kyari da Dr.Bulyaminu Gambo dai dama daga ciki da wajen Niger ne suka halarci taron ciki har da wasu Sarakunan gargajiya suka harlarci wajen taron.

Jigon taron shine gudunmuwar da yan jaridu zasu bayar wajen ingata zaman lafiya da hadin kai da kuma kwanciyar hankali ta hanyar harshen hausa tare da tabbatar da yancin kan kasashen Africa.

 

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...