Tsohon shugaban kwamitin kudi na Majalisar Wakilai, Faruk Lawan, ya bayyana hukuncin da aka yi masa na zaman gidan yari a matsayin ƙaddara.
Tsohon dan majalisar ya bayyana haka ne a jawabinsa yayin ziyarar da ya kai mazabar Shanono da Bagwai a ranar Asabar.
“Bayan kammala zaman gidan yari na kara zama mutum na gari, kuma ya gode wa Allah a kan komai”. Inji shi
Dangane da ziyara kuma, ya kuma ce, “wannan ziyara ba ta siyasa ba ce, ziyarar ta ta’aziyya da jajanta wa marasa lafiya da kuma girmama iyaye da shugabannin yankin ne”.
Kotu ta yankewa Faruk Lawan, hukuncin zaman gidan yari na shekaru bakwai saboda laifin karɓar cin hancin Dala miliyan uku a lokacin ya na shugaban kwamitin bincike na Majalisar Wakilai kan tsarin tallafin man fetur, daga hamshakin attajirin mai, Femi Otedola a shekarar 2012
Mai shari’a Angela Otaluka ta babbar botun FCT da ke Apo ta same shi da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume uku da hukumar ICPC ta shigar, ta kuma umarce shi da ya mayar da dala dubu 500,000 ga gwamnatin tarayya.
Ya kuma shaki iskar ‘yani ne ranar 15 ga watan Okbotar 2024 bayan shafe shekaru biyar a maimakon Bakwai da kotu ta yi umarni, sakamakon soke wasu tuhume-tuhume biyu daga ciki.