Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, yayi ikirarin yin duk mai yiwuwa domin ganin an kayar da jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027.
Atiku ya yi furucin ne a ranar Litinin bayan ya karɓi katin zamansa ɗan jam’iyyar ADC a mazabarsa ta Jada, Jihar Adamawa.
Tun a ranar 14 ga watan Yuli, Atiku ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.
Ya kuma ya ce PDP ta kauce daga ainihin harsashin da aka kafa ta a kai, wanda ta sa ya ga dacewar rabuwa da ita.
A jawabinsa bayan yin rajistar a ADC, Atiku ya ce matakin yin haka ya samo asali ne daga kishin kasa da muradin ganin Najeriya ta samu shugabanci nagari.
“Manufata ita ce ciyar da ƙasar gaba, tare da inganta walwalar al’umma idan ya samu damar zama shugaban kasa nan gaba”. In ji shi.
