Ƙungiyar ilimi ta Dawakin Tofa Academic Forum ta karrama fitattun mutane goma ’yan asalin ƙaramar hukumar, bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban al’umma, a bikin ranar jarumai na farko da ta shirya.
A jawabinsa na maraba, shugaban ƙungiyar, Dr Junaidu Danladi, ya ce shirya bikin na da muhimmanci wajen adanawa da tunawa da tarihi da gudunmawa da suka bayar ga al’umma, domin zaburar da yara masu tasowa su yi koyi da irin ayyukan da suka yi.
A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa,Anas Mukhtar Bello Danmaliki, ya godewa masu shirya taron da duk waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen nasararsa.
Shi ma shugaban taron, Surveyor Muhammad Nadu Yahaya, ya ce girmama irin mutanen zai zaburar da matasa wajen bayar da tasu gudunmawar ga ci gaban al’ummominsu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa bikin ya samu halartar uban taron, Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim Cigari, inda Dr Amir Abdulazeez ya karanta tarihin waɗanda aka karrama, tare da bayyana nasarorinsu da gudunmawar da suka bayar.
