
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma jigo a jama’iyyar ADC Atiku Abubakar, ya bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa kan shugaban kasa Bola Tinubu da ministocinsa.
Atiku ya yi kira ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a safiyar Laraba.
Atiku ya fadi haka ne bayan murabus ɗin ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, da ake zargin ya gabatar da takardar karatu na bogi.
“Murabus ɗin Uche Nnaji daga mukaminsa na Ministan Kimiyya da Fasaha yunƙurin ɓoye abin kunya da ke cikin gwamnatin Tinubu ne”.
Wannan abin kunya ne kuma ya nuna cewa akwai matsalar gaskiya da amana a cikin gwamnatin Tinubu tun daga sama har ƙasa.