An yi jana’izar manoma 26 da aka kashe a wani hari da ’yan bindiga suka kai a Jihar Zamfara, kamar yadda wata sanarwa daga hukumomi suka tabbatar.
Hukumomin yankin sun ce an kai wa manoman harin ne a ranar Alhamis, yayin da suke aiki a gonakinsu da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda a jihar ta Zamfara.
Kisan ya sake jefa fargaba a zukutan manoma, inda da dama daga cikinsu suka daina zuwa gonakinsu saboda ci gaba da hare-haren da ƙungiyoyin ’yan bindiga masu ɗauke da manyan makamai ke kai wa a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
Yayin wata ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar da abin ya shafa a madadin Gwamna jihar Zamfara Dauda Lawal, Mataimakin Gwamnan Zamfara, Mani Malam Mummuni, ya buƙaci mazauna yankin su ƙara haƙuri, yana mai cewa gwamnatin jihar na ci gaba da jajircewa wajen kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
A watan Yuni, aƙalla manoma 17 aka kashe, yayin da wasu 13 suka jikkata lokacin da aka kai musu hari a gonakinsu Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.
Harin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mazauna yankin 39 da suka taru domin tattaunawa kan yadda za a sako ’yan uwansu da aka sace.
Tun da farko a watan, wani hari da aka kai ƙauyen Gora, shi ma a Ƙaramar Hukumar Maradun, ya yi sanadin mutuwar manoma shida, tare da jikkata kusan mutum 10 da kuma yin garkuwa da wasu mazauna yankin
