
Kayar da Atiku Abubakar a zaben fidda gwani na takardar Shugaban kasa a jam’iyyar ADC zai yi wahala.
Sanata Shehu Sani ne ya fadi hakan, yana mai cewa, Atiku yana da karfin gaske a cikin jam’iyyar saboda yawan goya bayansa da tsarin siyasarsa, da kuma tasirinsa a fadin kasar.
“Zaben fidda gwani ba a kan gama-garin jama’a ake yinsa ba, kuma Atiku zai iya samun kuri’u mafi yawa a zaben jam’iyyar ADC, inda yake tare da Peter Obi da kuma karin wasu.
“Atiku yana da karfi wajen samun nasara a zaben fidda gwani, musamman saboda kudi da tsarin siyasa.
“Obi ba zai iya samun nasara ba sai dai wani ikon Allah ko kuma idan Atiku ya janye.” In ji shi.
Sani ya kuma ce, Atiku ya tsaya takara sau shida, yana da karfin cin zaben fidda gwani saboda tsarinsa da kwarewarsa.
Sai dai ya yi gargadin cewa zabin Atiku na iya kawo cikas ga jam’iyyar a zaben gama gari saboda batun juyar da mulki zuwa Kudu.