Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, zai gana da shugaban Amurka, Donald Trump, a yau Talata don tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza.
Trump ya yi alkawarin kawo karshen watanni 15 na yaki tsakanin Isra’ila da Hamas, inda aka saki ƴan Isra’ila 13, ƴan Thailand 5, da Falasɗinawa 583 daga gidajen yari.
Netanyahu ya bayyana cewa yarjejeniyar na wucin-gadi, yana mai cewa Isra’ila na da “yancin sake komawa yaƙar” Hamas tare da goyon bayan Amurka.
Idan an samu daidaituwa, za a saki ƴan garkuwa 33 da Falasɗinawa 1,900 daga gidajen yari.