Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta yaba wa kokarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da rayuwar al’ummar Borno bayan tashe-tashen hankulan Boko Haram.
Shugaban tawagar EU a Borno, Ambasada Gautier Mignot, ya bayyana hakan yayin ziyarar da suka kai cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna.
Cibiyar na horar da matasan da rikicin ya shafa, musamman wadanda suka fuskanci tasirin Boko Haram.
Mignot ya ce tawagar ta gamsu da irin damar da cibiyar ke bai wa al’ummar jihar.
Tawagar ta kuma ziyarci gidan Gwamnati, inda ta jaddada kudirin EU na hadin gwiwa da gwamnatin Borno.
Hadakar za ta taimaka wajen samar da zaman lafiya tare da hukumar hadin kan kasa da kasa ta Jamus.
