Hukumar Hisbah a nan Kano ta fara gudanar da shirin Auran gata na mutum Dubu uku da gwamnatin Kano ta shirya, inda ta bawa Ango da Amarya kayan da zasu saka da certificate.
Mataimakin kwamandan hukumar Mujahid Aminuddin ne ya bayyana hakan a yau litinin, yayin Yarabon kayan na Amarya da Ango a hedikwatar hukumar dake Sharada.
Mujahid Aminuddin yace za’a gudanar da daurin Auran a ranar Juma’a me zuwa a babban masallacin juma’a na cikin gari.
Wasu daga cikinra angwaye da amaran da suka karbi kayansu sun nuna farin cikin su da godiya ga gwamnatin Kano kan wannan gudummawar da taba su.
Hukumar Hisba tayi kira ga angwaye da amare da su tabbatar sun zo da certificate da kayan shaidar aure da aka basu ranar daurin auren.
