Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima ya ce yawan yara marasa zuwa makaranta a kasar nan, barazana ce da ke buƙatar haɗin gwiwa daga dukkanin matakan gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki.
Sanata Shettima ya bayyana hakan a lokacin a taron Zauren Ilimin kasar nan na shekarar 2025 wanda aka gudanar a birnin tarayyar Abuja, wanda Kungiyar Gwamnonin Najeriya da kuma Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da abokan hulɗa suka shirya.
Nan ba da jimawa ba zamu kawo karshen matsalar tattalin arziki – Kashim Shettima
Gwamnatin Kano ta ware miliyan 242 domin gyara makarantar Government Technical Danbatta.
Ya kuma yi kira da a faɗaɗa ilimin sana’o’i da kuma fasaha domin matasa su samu ƙwarewar da za ta taimaka musu a kasuwa ta yadda za’a rage yawaitar marasa aiyukan yi a fadin kasar nan.
Sanata Kashim Shettima ya jaddada cewa gina tsarin ilimi mai ɗorewa na buƙatar haɗin gwiwa daga kamfanoni masu zaman kansu, shugabannin masana’antu, ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai da kuma tallafin al’umma.
