Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Izge da ke Karamar Hukumar Gwoza a jihar Borno,
Rahotanni na cewa harin ya auku ne da misalin karfe 1:00 na ranar Lahadi a lokacin da ƴan ta’addan suka mamaye sansanin sojin Najeriya da ke garin Izge.
Wata majiyar tsaro ta tabbatarwa jaridar Daily Trust cewar Wani soji mai mukamin Kyaftin da kuma Kofur na daga cikin wadanda suka mutu, yayin da sojojin suka yi nasarar hallaka maharan da dama a yayin arangamar.
Shaidu sun ce maharan da dama kan babura ne suka mamaye sansanin sojojin suka kuma yi ta harba makamin roka da ake kira RPG.
Sai dai daga bisani mafarauta da ‘yan banga sun kawo wa sojojin dauki tare da kara musu kwarin guiwa har ta kai ga fatattakar ƴan ta’addan da suka tsere zuwa dajin Sambisa.
