Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta ce, akalla bakin haure 53 ne suka mutu ko suka ɓace bayan da wani jirgin ruwa na roba dauke da mutane 55 ya kife a gabar tekun Libya.
Hukumar ta wata sanarwa da ta fitar ta ce mata ‘yan Najeriya biyu ne kawai aka ceto a lokacin wani aikin ceto da hukumomin Libya suka yi.
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijirar ta ce jirgin ya kife a cikin tsakiyar Tekun Bahar Rum, arewacin garin Zuwara, a karshen mako.
- Lebanon ta saki dan Gaddafi bayan shekaru 10 da tsare shi
- Jirgin Ruwa Ya Kife Da Ƴan Gudun Hijira a Gabar Tekun Yamen.
- Najeriya ta mayar da bakin haure ‘ƴan Mali 62 kasarsu
A cewar IOM, ‘yar Najeriya da ta tsira ta ce mijinta ya nutse, yayin da ɗayar ta ce ‘ya’yanta biyu sun mutu.
Wadanda suka tsira sun bayyana cewa jirgin yana dauke da bakin haure da ‘yan gudun hijira daga wasu kasashen Afirka da dama.
IOM ta yi gargaɗin cewa wannan shine karo na baya-bayan nan da jirgin ruwan ya nutse a lokacin mummunan yanayi na hunturu.
A ƙarshen watan Janairu, hukumar ta taimaka wa ‘yan ci-rani ‘yan Najeriya 177 komawa gida a wani jirgin sama na agaji .
Hukumar ta sake sabunta kira ga ƙarin haɗin gwiwa na ƙasashen duniya domin samar da hanyoyin kariya ga masu yin hijira.
