Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta samu nasarar kashe wata gobara da ta tashi a kasuwar Briged wanda hakan ya hana yaduwarta.
Gobarar wacce ta ci wasu shagunan kasuwar a ‘Yan-Katako ta an samu nasarar kasheta cikin gaggawa.
Kakakin hukumar Saminu Yusuf Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar ya ce, ma’aikatan hukumar daga ofishin Bompai ne suka samu isa wurin kana lokaci suka kuma kashe wutar.
Wanda hakan ya sa ba samu hasarar rai ko dukiya mai yawa ba a gobarar.
An danganta tashin gobarar da dawo da wutar lantarki da aka yi a inda ta kama daya daga cikin na’urorin lantarkin da ke cikin shagon.