Ana zargin Ƴan bindiga da kashe wani fitaccen ɗansiyasa a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Alhaji Umar S Fada Moriki na ɗaya daga cikin jiga-jigan ƴansiyasar jihar.
Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne ranar Asabar da safe a kan babban titin Gusau zuwa Tsafe, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Gusau.
- Yaki da ‘yan bindiga: Gwamnan Kano ya ba sojoji motoci 10 da babura 60
- ‘Yan bindiga sun yiwa Hakimi yankan rago a Zamfara
- Cikin Mako Guda Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 24, Sun Sace 144 a Zamfara – Zamfara Circle
Cikin wata sanarwa da jam’iyyar APC reshen jihar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Yusuf Idris ya ce marigayin ya gamu da ajalinsa ne bayan halartar taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, wanda ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle ya jagoranta.
Mai shekara 62 ya taɓa rike mukamin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zurmi, sannan ya riƙe muƙamin babban darakta a wata hukuma kafin ya zama mataimakin gwamna na musamman kan samar da lantarki a karkara.
A zaɓukan 2023 da suka gabata ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar ƙananan hukumomin Zurmi da Shinkafi.
