
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya shawarci sauran gwamnonin Arewacin Najeriya su ɗauki cikakken nauyin tsaron jihohinsu, yana mai cewa babu wani dalili na gaza ɗaukar matakai a yanzu ganin yadda kuɗaɗen da ake rabawa daga Abuja suka ƙaru fiye da da.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin.
“Wannan lokaci gwamnatin tarayya ta raba sama da naira tiriliyan biyu da miliyan dari biyu ga jihohi, wanda ya ninka duk wani adadi da aka saba rabawa a baya.
“Bai kamata gwamnoni su dora alhakin matsalar tsaro kan wani ba. Ya kamata su zargi kansu, domin yanzu kowace jiha tana da isassun kuɗaɗe da za ta iya kare jama’arta,” in ji Gwamna Sule.