Sama da rabin miliyan na mutanen da ke zaune a yankunan kan iyakar Cambodia da Thailand sun bar gidajensu sakamakon tsanantawar yaƙi tsakanin ƙasashen biyu dake yankin Asiya.
A jiya Laraba, an ci gaba da musayar wuta da manyan makamai, inda mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Thailand ya ce an kwashe fararen hula sama da dubu 400 daga yankin saboda dalilai na tsaro.
A bangaren Cambodia, rundunar sojin ƙasar ta tabbatar da kwashe mutane fiye da dubu 100, yayin da dakarun ƙasashen biyu ke amfani da jiragen yaƙi, tankoki, da jirage marasa matuka domin kai wa juna farmaki.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi alƙawarin gudanar da tattaunawa ta wayar tarho da shugabannin Thailand da Cambodia domin neman tsagaita wuta.
Rikicin ya samo asali ne daga rashin jituwa kan mallakar wasu yankunan iyaka, inda lamarin ya fara ƙazancewa tun shekarar 2008, kuma yanzu ya kai ga amfani da karfin soja kai tsaye.
